Sa’o’i 8 da suka wuce
Wasu ɗaliban Najeriya ƴan asalin jihar Zamfara waɗanda ke karatu a fannoni daban-daban a Cyprus, sun koka da yadda suka ce gwamnatin jihar ta watsar da su ba tare da biyan kuɗaɗen karatun su ba.
Ɗaliban sun shaidawa BBC cewa yanzu haka basu san matsayar karatun su ba, saboda makarantarsu ta gaji da jiran a biya masu kuɗin karatu daga ɓangaren gwamnati har sun dakatar da su, lamarin da ya jefa da dama a cikin su cikin mawuyacin halin rayuwa.
Daliban dai musamman mata, da wasun su suka shafe shekaru a ƙasar, sun bayyana halin talauci da rashin damar zuwa asibiti baya ga tsangwama da suke fuskanta, tsawon shekaru, abinda hakan ke barazanar jefa wasun su aikata ba daidai ba.
Sun ce yanzu haka suna fuskantar barazanar kora daga ƙasar saboda takardunsu na neman izinin tafiya sun lallace kuma babu halin yin wasu.
Ɗaya daga cikin ɗaliban ya shaidawa BBC cewa ‘‘Tun a lokacin tsohon gwamna, Dr Bello Matawalle aka buɗe scholarship muka ciika, aka dauke mu, aka kawo mu karatu a ƙasar Cyprus mu 93, to wahalolinrayuwa ya sa mun dawo mu 88.
‘‘An bin gwamnati bashin kuɗin karatunmu, hukumar makaranta ta yi haƙuri har ta gaji. Sannan idan ka dawo maganar kudin abinci, tun 2022 gwamnatin Zamfara ba ta ƙara bamu kuɗin abinci ba.’’
Galibin daliban, da ke karatun fannonin ilmin hada magungunna, da na ɓangaren makamashi da sauran su, sun ce an raba su da iyayensu shekara biyar kenan, ga kuma rashin sanin tabbas game da makomar karatunsu, a cewar wannan dalibar.
‘‘Haka muke zaune, iyayenmu suke ƙoƙarin taimaka mana ɓangaren kuɗin abinci, musamman mu mata, duk da dai ba wani ƙarfi iyayen namu ke da shi ba, amma suna ƙoƙari su turo mana abinda za mu siya abinci.
‘‘Mun bi duk hanyoyin da ya kamata mu bi amma har yanzu abubuwa ba su daidaita ba. Mun yi missing semesters guda biyu, sheekara guda kenan, ga ita ma wagga semester har an yi nisa . ka ga idan bamu yi ta ba, shekara biyu kenan’’
Ɗalibar ta ƙara da cewa saboda tsananin fargaba da suke ciki ‘‘Ko rashin lafiya mutum ya ke yi ba ya iya zuwa asibiti. Kusan shekara biyar kenan tun da muka baro gida ba mu je ba, ka ga itama wata babbar damuwa ce a gare mu’’
BBC ta tuntuɓi gwamnatin jihar Zamfara a kan wannan batu, inda Malam Sulaiman Bala Idris mai magana da yawun gwamnan jihar, ya ce su na sane da halin da ɗaliban ke ciki, kuma matsala ce da suka gada, amma yanzu haka suna kokarin daukar matakan gaggawa domin taimakawa ɗaliban.
‘‘Matsala ce wadda ta samo asali tun daga gwamnatin da ta gabace mu, matsaloli ne marasa daɗi kuma marasa kyau. Tun kafin mu zo gwamnati ta yi watsi da su.’’ Inji Malam Sulaiman Bala Idris.
Mai magana da yawun gwamnan ya kuma ƙara da cewa ‘‘Cikin ƴan kwanakin nan, gwamnatin Zamfara za ta kai masu ɗauki, kuma za ta biya duk kuɗaɗen da ake neman’’
A lokacin gwamnatin Bello Muhammad Matawalle ne aka tura daliban domin karo ilmi, abinda jama’a ke zargin tamkar wannan gwamnati ta bar su ne cikin wannan yanayi saboda siyasa.
A Najeriya dai an sha samun gwamnatoci da ke tura dalibai a kasashen waje da sunan karatu amma daga bisani idan an samu sauyin gwamnati a watsar da su ba tare da la’akari da muhimmancin abinda za su karanta ba.