Al’amarin ya ja hankalin ‘yan sanda ne a shekarar da ta gabata lokacin da wata mata ta shigar da korafi, inda da fari ta yi ikirarin cewa an yi mata sata.
Sai dai, a yayin yi mata tambayoyi, aka fahimci cewa an yo safararta ne da nufin yin karuwanci.
Da aka zurfafa bincike, an tabbatar da hakan, sannan aka sauyawa matar wuri zuwa wani amintaccen gida, a cewar kakakin rundunar ‘yan sandan kasar Christos Andreou.
Binciken ya dauki lokaci ne saboda karancin bayanan da matar take dasu game mutanen dake cin zarafinta, a cewar Andreou.
Kokarin jami’an ‘yan sanda ya kai ga kama wata mata mai shekaru 44 a ranar 9 ga watan Oktoban da muke ciki, da ake zargi da hannu a harkar safarar mutane, sai kuma kamen daya biyo baya a ranar 18 ga watan Oktoban da muke ciki, sannan an kama mace ta 3, mai shekaru 33.
Har yanzu ana neman wasu maza 2 dangane da lamarin.
Andreou ya kara da cewa ‘yan sanda sun tara wadatattun hujjoji kuma ana sa ran zasu gabatar da batun a gaban kotu nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.